Ana ci gaba da fiskantar rikici a Thailand
May 17, 2010Talla
Arangama na ci gaba da gudana tsakanin masu ƙin jinin gwamnatin Thailand da kuma dakarun wannan ƙasa da ke neman dawo da doka da oda. A kalla fararen hula 35 suka mutu ya zuwa yanzu a faɗan da ya ɓarke tsakanin masu adawa da gwamnatin da Jami'an tsaro.
Rikicin dai ya mamaye birnin na Bangkok da kewaye, inda ya zuwa yanzu ake cigaba da fito na fito tsakanin dakarun gwamanti da kuma magoya bayan tsohon firaminista.
Gwamantin ta Thailand ta na ci gaba da karfafa martaninta kan masu zanga-zangar, tare da ƙin amincewa da shiga tattaunawar da Majalisar Ɗunkin Duniya za ta jagoranta, domin kawo ƙarshen rikicin daya shiga yini na huɗu.
Mawallafi: Mouhamadou Awal Edita: Abdullahi Tanko Bala