1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana ci-gaba da gwabza fada a Sri Lanka

August 5, 2006
https://p.dw.com/p/Bunn
Tashin bomb a iraki
Tashin bomb a irakiHoto: AP

Dakarun gwamnatin Sri Lanka sun ce sun mayar da martani na wani harin ´yan tawayen Tamil Tigers a kusa da wani gari mai tashar jiragen ruwa dake arewa maso gabashin kasar, inda suka halaka ´yan tawaye 35. Ana kuma ci-gaba da gwabza kazamin fada a garin Muttur inda majiyoyin kungiyoyin agaji suka ce an yiwa mutane sama da dubu 20 kofar rago cikin kwanakin nan. Yanzu haka dai mutane dubu 7 daga garin sun isa Kantalewanda ke hannun dakarun gwamnati. Amma har yanzu wasu dubu 17 na kokarin tserewa daga garin na Muttur. A kuma halin da ake ciki gwamnatin kasar Norway ta ce wani mai yin sulhu na kasar ya isa tsibirin Jaffna dake arewacin Sri Lanka inda tattauna da ´yan tawayen Tamil Tigers. Wani labarin da ya iso mana yanzu yanzu kuma na cewa an kashe ´yan tawaye 152 a arewa maso gabashin kasar lokacin da dakarun gwamnati ke kokarin kwace wani garin al´umar musulmi mai tashar jirgin ruwa.