1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana ci-gaba da kai hari a kan ´yan shi´a a Iraki

April 8, 2006
https://p.dw.com/p/Bv2d
A dangane da hare haren da ake kaiwa kullum akan mabiyya darikar shi´a da kuma barazanar daukar fansa akan ´yan sunni musamman akan masallatansu a Iraqi, shugabannin kasar na gargadi game da barkewar yakin basasa a cikin kasar. A lokacin da yake jawabi a gaban wani taro gangami, shugaban babbar jamiyar ´yan shi´a a Iraqi, Abdel Aziz Hakim ya yi kira ga magoya bayansa da su kai zuciya nesa. Hakim ya ce bai kamata ´yan takife masu ta da zaune tsaye su yi nasara haddasa wani yaki tsakanin al´umomin Iraqi ba. Shi kuma a lokacin da yake yin Allah wadai da jerin hare haren babban sakataren MDD Kofi Annan cewa yayi jerin hare haren na nuni ne da muhimmancin dake akwai wajen gaggauta hadin kan kungiyoyin addinan kasar don kafa sabuwar gwamnati. A ci-gaba da tashe tashen hankula a cikin Iraqin kuwaa a yau ma mutane 5 sun rigamu gidan gaskiya sakamakon wani harin bam da aka kai da mota akan wani wurin ibadar ´yan shi´a dake Musayyib. A jiya juma´a mutane 79 suka rasu a hare haren da aka kan wani masallacin ´yan shi´a dake birnin Bagadaza.