1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana ci gaba da kamen 'yan adawa a Ruwanda

Gazali Abdou Tasawa
September 7, 2017

'Yan sanda a birnin Kigali sun kame bakwai daga cikin shugabannin wasu jam'iyyun siyasa biyu na bangaren adawa da ba su da rijista ciki har da jam'iyyar FDU-Inkingi ta Victoire Ingabire da ke tsare ba tun yau ba.

https://p.dw.com/p/2jWUm
Unterzeichnung Friedensabkommen im Kongo
Hoto: Reuters

Rahotanni daga kasar Ruwanda na cewa 'yan sanda a birnin Kigali sun kame bakwai daga cikin shugabannin wasu jam'iyyun siyasa biyu da suka hada da jam'iyyar FDU-Inkingi ta 'yar adawar kasar Victoire Ingabire da tsare .

 A cikin wata sanarwa da kakakin jam'iyyar ta FDU-Inkingi ya fitar a wannan Alhamis a birnin London inda yake zaman gudun hijira ya yi tir da Allah wadai da kamen da mahukuntan Ruwandar suka yi a ranar Laraba na wasu shika-shikan jam'iyyar uku da suka da mataimakin shugaban jam'iyyar. 

Ita ma dai jam'iyyar PDP-Imanzi ta sanar da cewa 'yan sanda sun kame shugabanta Jean-Marie Kayumba a birnin Kigali. Sai dai daga nata bangare hukumar 'yan sandar birnin na Kigali ta ce mutanen da ta kama, mutane ne da ke da alaka da wata kungiyar tawayen kasar da ke da cibiyarta a wata kasa makwabciya.