1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana ci gaba da kara samun tashe-tashen hankulla a kasashen musulmi, dangane da zanen hotunan batancin nan da aka yi wa annabi Muhammadu, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.

February 8, 2006
https://p.dw.com/p/Bv8t

Kungiyar kasashen musulmi , ta shiga sahun manyan kafofi na duniya kamarsu Kungiyar Hadin Kan Turai da Majalisar Dinkin Duniya, wajen yin kira ga musulmi da su kwantad da hankalinsu, su kuma kawo karshen tarzomar da suke yi ta nuna bacin ransu ga zanen hotunan wulakancin nan da aka buga, masu nuna batanci ga annabi Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi. A cikin wata sanarwar da ta buga, kungiyar, wadda ta kunshi kasashe mambobi 57 na duniya, ta ce kai hare-hare kan jama’a da kadarorinsu na shafa wa suna addinin islama kashin kaza. Sanarwar dai ta biyo bayan ci gaba da zanga-zanga da tarzomar da ake ta yi ne a yankuna daban-daban na duniyar musulmi.

A kasar Afghanistan, rahotanni sun ce Majalisar Dinkin Duniya ta janye jami’anta daga garin Maymana, bayan da masu zanga-zanga suka kai hari kan wani sansanin kungiyar NATO, inda aka tsugunad da sojojin kasar Norway. A wata sabuwa kuma, mutane 4 ne rahotannnin suka ce sun rasa rayukansu, sa’annan wasu 18 kuma suka ji rauni, yayin da `yan sandan Afghanistan din suka bude wa masu zanga—zangar wuta.