1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana ci-gaba da matsawa yara shiga aikin soji a gabashin Kongo

December 24, 2007
https://p.dw.com/p/Cfgm

Wata ƙungiyar agaji mai mazauni a ƙasar Birtaniya ta ce sabbin tashe tashen hankula a gabashin Kongo ya haddasa ƙaruwar ɗaukar ƙananan yara aikin soji. A cikin wata sanarwa da ya bayar shugaban ƙungiyar a Kongo, Hussein Mursai ya ce mayaƙan dukkan bangarorin dake faɗa suna amfani da yara maza da mata a filin daga, inda suke tilasta musu ɗaukar makami ko kuma yin lalata da su. Kungiyar ba ta faɗi yawan yaran da abin ya shafa ba. tun bayan kawo karshen yaƙin basasan ƙasar na shekaru biyar a shekara ta 2003, yankin gabashin kasar ta Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo ya zama wani dandanlin rashin bin doka da oda.