1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana ci gaba da neman hanyoyin ceto tattalin arzikin Girka

Suleiman BabayoJune 27, 2015

Firaministan Girka Alexis Tsipras ya kira zaɓen raba gardama kan magance matsalolin tattalin arziki, yayin da ministoci kuɗi na ƙasashen ke ci gaba da taro

https://p.dw.com/p/1FoLy
Griechenland Schuldenkrise lange Schlangen vor Geldautomaten
Hoto: Getty Images/AFP/S. Mitrolidis

Hukumar ba da lamuni ta duniya, IMF ta ce za ta ci gaba da aiki domin kare tattalin arzikin ƙasar Girka. Shugabar hukumar Christine Lagarde ta faɗi haka, jim kaɗan bayan firaministan ƙasar ta Girka ya kira ƙuri'ar raba gardama kan amince ko watsi da yarjejeniyar bai wa ƙasar rance. Lagarde ta shaida wa manema labarai a birnin Brussels na ƙasar Belgium babban ɓuri ne ceto tattalin arzikin ƙasar ta Girka.

Firaminista Alexis Tsipras ya nemi 'yan ƙasar su yi zaben raba gardama a wani jawabi. Mahukuntan na birnin Athens za su nemi fadada shirin taimaka wa tattalin arzikin ƙasar zuwa fiye da ranar Talata mai zuwa, domin 'yan kasar ta Girka su kada kuri'ar raba gardama kan amincewa ko watsi da yarjejeniyar ceton tattalin arzikin ƙasar. Za a gudanar da zaben raba gardama ranar biyar ga wata gobe na Yuli. A wannan Asabar ministoci kudi na ƙasashe masu amfani da kudin bai daya da Euro na ci gaba da tattaunawa kan batun.