1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana ci gaba da neman sako yan Burtaniya da akayi garkuwa dasu a Habasha

March 4, 2007
https://p.dw.com/p/BuQg

Har yanzu ana ci gaba da neman wasu yan kasar Burtaniya 5 da aka sace a kasar Habasha.

Yan Sandan kasar sunce an sace turawan ne masu yawon bude ido tare da wasu direbobin Habashan da dama da kuma wasu masu tafinta ga turawan 5 a lardin Afar dake arewa maso gabashin babban birnin kasar Addis Ababa.

Cikin wadanda aka sacen akwai maaikatan ofishin jakadancin Burtaniya.

A yanzu haka an aike da wata tawaga ta jamian Burtaniyan domin taimaka sako wadannan mutane.

Jamian kasar Habashan dai sun zargi dakarun kasar Eritrea makwabciya da laifin sace turawan,zargi da tuni kuma Eritrea ta karyata.