1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana ci gaba da samun hauhawar tsamari a garin Jericho a gaɓar Yamma, bayan ɗaukin da dakarun Isra’ila suka yi na kame wani madugun `yan ta kifen Falasɗinawa.

March 15, 2006
https://p.dw.com/p/Bv51

Cafke wani shugaban `yan ta kifen Falasɗinawa da ƙarfin soji, a wani kurkukun da ke garin Jecho a Gaɓar Yamma jiya, da dakarun Isra’ila suka yi, ya haddasa jerin tashe-tashen hankulla a yankin. Rahotannin da muka samu sun ce, matasan Falasɗinawa sun kai hare-hare kan kadarorin Ƙungiyar EU da kuma na Amirka da ke yankin, sun kuma yi garkuwa da baƙi da dama. Sai dai a halin yanzu, rahotannin sun ce, an cim ma sako duk baƙin, ban da wasu mutane guda uku.

Isra’ila ta afka wa gidan yarin ne, don ta cafke Ahmed Saadat, wanda ake zargi da shirya kisan gillar da aka yi wa wani ministan Isra’ila a shekara ta 2001. Game da harin dai, shugaban Falasɗinawa Mahmoud Abbas, ya dakatad da ziyarar da yake kaiwa a nahiyar Turai, ya koma gida, inda ya yi kira ga al’ummansa da su kwantad da hankalinsu.

Shugaban Majalisar Tarayyar Turai ya yi tofin Allah Tsine ga Isra’ila game da harin da ta kai a gidan yarin da kuma garkuwar da aka yi da baƙi, bayan wannan ɗaukin. Falasɗinawan dai sun afka wa wasu cibiyoyin Birtaniya da na Amirka da ke yankin ne, saboda masu sa ido daga ƙasashen biyu, sun fice daga gurabansu da ke gidan yarin na Jericho ne, jim kaɗan kafin ɗaukin dakarun Isra’ilan.