1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana ci-gaba da samun tangarɗa a zurga-zurgar jiragen sama a Turai

April 17, 2010

Har yanzu gajimaren toka na ci-gaba da kawo cikas a zurga-zurgar jiragen sama

https://p.dw.com/p/Myrp
Fasinjoji za su ci gaba da jiran tsammani warabbuka a filayen jiragen samaHoto: AP

Ɗaukacin nahiyar Turai na ci-gaba da zama wani wurin da aka hana zurga-zurgar jiragen sama yayin da gajimaren toka daga wani dutse dake amar wuta a ƙasar Iceland ke ci-gaba da tirniƙe sararin samaniyar Turai. Hukumomin kula sufurin jiragen sama a ƙasashen Turai da dama na tsammanin za a ci-gaba da soke tashi da saukan jiragen sama a yau Asabar. Yanzu haka dai an rufe dukkan filayen jiragen sama 16 a Jamus, sannan filayen jiragen sama a ƙasashen Faransa, Birtaniya da kuma Netherlands za su kasance a rufe a yau. An kiyasce cewa wannan matsalar na jawowa kamfanonin zurga-zurgar jiragen saman da abin ya shafa, asara dala miliyan 200 a kowace rana. A kuma halin da ake ciki Kwamitin Sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce ya soke wata tafiya da ya shirya zuwa Janhuriyar Demokuraɗiyyar Kongo yana mai nuni da taɓarɓarewar zurga-zurgar jiragen saman a ƙasashen Turai.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal

Edita: Abdullahi Tanko Bala