1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana ci-gaba da shawarwarin zaman lafiyar Darfur a Abuja

May 3, 2006
https://p.dw.com/p/Buzl

Masu shiga tsakani na kungiyar tarayyar Afirka sun sake kara wa´adi don cimma wata yarjejeniya a shawarwarin samar da zaman lafiyar lardin Darfur dake gudana yanzu haka a Abuja babban birnin tarayyar Nijeriya. Yanzu haka an bawa masu tattaunawa wa´adin zuwa ranar alhamis daddare da su cimma yarjejeniya tsakanin gwamnatin Sudan da ´yan tawaye. An dakatar da kulla yarjejeniyar ce saboda korafin da ´yan tawaye suka yi cewar ka´i´dojin yarjejeniyar ba su biya bukatunsu na raba madafun iko da kuma raba albarkatun man fetir ba. Amirka da Birtaniya sun aika da manyan jami´an diplomasiyar su zauren shawarwarin a Nijeriya da zumar taimakawa a cimma yarjejeniya, wadda zata kawo karshen rikicin da aka shafe shekaru 3 ana yi a Darfur, wanda yayi sanadiyyar rayukan mutane kimanin dubu 200.