1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana ci-gaba da taron kolin kasashen nahiyar Amirka a Argentina

November 5, 2005
https://p.dw.com/p/BvMR

Shugabannin kasashen nahiyar Amirka na ci-gaba da taron kolin da suke yi a birnin Mar del Plata na kasar Argentina duk da jerin zanga-zanga da tashe tashen hankula da suka dabaibaye taron. Zanga-zangar dai ta nuna adawa ne tare da sukar manufofin shugaba GWB na Amirka musamman dangane da shirinsa na kafa wani yankin ciniki maras shinge tsakanin kasashen nahiyar Amirka gaba daya. To sai dai babban jigon taron kolin shi ne daukar matakan yaki da matsalolin marasa aikin yi da kuma na talauci da suka yiwa daukacin kasashen yankin katutu. Masu zanga-zangar sun kai harin bam akan reshen bankin nan na Citibank dake birnin Rosario sannan ´yan sanda da dama sun jikata sakamakon wani artabu da suka yi da masu zanga-zanga. Sannan kuma a Buenos Aires babban birnin Argentina wasu sun jefa irin bam din na kwalaba akan wuraren sayar da abinci na tafi da gidanka da kuma kan wani bankin Amirka.