1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana ci-gaba da taron mashawartar Majalisar Dinkin Duniya

September 20, 2006
https://p.dw.com/p/Buim
A yau aka shiga rana ta biyu a taron shekara shekara na babbar mashawartar MDD dake birnin New York. Daga cikin shugabannin da suka yi jawabi a yau har da shugaban Afghanistan Hamid Karzai wanda ya ce ayyukan ta´addanci na karuwa a cikin kasar sa. Shi kuwa a jawabin sa shugaban Venezuella Hugo Chavez ya kira shugaban Amirka GWB ne da cewa shi ne babban shaidani kuma dan mulkin kama karya a duniya. Shugaba Chavez ya fadawa babbar mashawartar cewa kanekanen da manyan kasashe suka yiwa kwamitin sulhun ya sa yanzu MDD ba ta da wani amfani kuma tuni an kauce daga manufofin da suka sa aka kirkiro majalisar bayan yakin duniya na biyu. A martanin farko da ya mayar ga jawabin na Chavez, jakadan Amirka a MDD John Bolton ya ce ba zai tofa albarkacin bakinsa ga abin da ya kira jawabi na shakkiyanci ba.