1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana ci gaba da zanga zanga a Ivory Coast

Hauwa Abubakar AjejeJanuary 18, 2006

Kwana uku a jere,matasa a kasar Ivory Coast sun tare manyan tituna a birnin Abidjan,yayinda kasashen duniya suke kara matsin lamba ga shugaba Laurent Gbagbo ya kawo karshen zanga zanga da magoya bayansa sukeyi don neman janyewar dakarun Majalisar Dinkin Duniya.

https://p.dw.com/p/Bu2L
Hoto: AP

Kasar ta Ivory Coast da tafi kowace kasa noman koko a duniya,ta tsinci kanta cikin tashe tashen hankula da zanga zangar nuna adawa da Majalaisar Dinkin Duniya a kudancin kasar dake karkashin gwamnatin Gbagbo.Yammacin kasar dai na a hannun yan tawaye tun yakin basasa na 2003 da ya dare kasar gida biyu.

Magoya bayan gwamnatin sun fara zanga zanga cikin wannan makodo don nuna adawarsa ga kira da masu shiga tsakani na Majalisar Dinkin Duniya suka yi na rushe majalisar dokokin kasar wacce magoya bayan Gbagbo suka fi yawa cikinta.

Tuni dai sakatare janar na Majalisar Kofi Annan ya kira gwamnatin Gbagbo data kawo karshen wannan zanga zanga da ya kira shiryayya don kin jinin Majalisar.

Babban hafsa mai kula da harkokin tsaro na Faransa,Henri Bentegeat ya baiyana imaninsa cewa yanzu lokaci ne da ya kamata kasashen duniya su lakabawa Ivory Coast takunkumi don nuna goyon bayansu ga shirin zaman lafiyar,yace tun da dadewa dama komitin sulhu yayi gargadin cewa,ya kamata a lakabawa kasar takunkumi.

Yace shugabannin kasashen duniya sun fara nuna gajin hakurinsu da halin da ake ciki a Ivory Coast,inda yanzu haka dakarun kasar Faransa 4,000 suke gudanar da aiyukan wanzar da zaman lafiya tare da takwarorinsu na Majalisar Dinkin Duniya fiye da 7,000.

Shugaba Laurent Gbagbo da farko ya shirya gudanar da taron manema labarai a yau laraba amma daga bisani ya janye taron.

A yau din dai a birnin Abidjan matasa sun ci gaba da tsayarda motoci suna bincikensu tare da neman takardun shaida na jamaa.Babu motocin haya a yawancin titunan birnin da yayi kaca kaca da dattin zanga zangar jiya.

A hedkwatar Majalisar Dinkin Duniya inda daruruwan magoya bayan gwamnati sukayi mamaye a jiya,kimanin matasa 300 sun koma a yau din.

Majalisar Dinkin Duniya da masu shiga tsakani na kasa da kasa dai suna kokarin ganin an kaddamar da shirin zaman lafiya da karkashinta zaa gudanar zaben shugaban kasa a watan oktoba bayan kwance damarar yaki.

Shekara guda da ya wuce kuma komitin sulhu ya jefa kuriar amincewa da kafa takunkumi akan Ivory Coast,wadda ya hada da haramta tafiye tafiye da dakatar da kadarorin wadanda suke hana ruwa gudu ga shirin zaman lafiya na kasar,amma bai kaddamar ba duk da cewa komitin ya sabunta wannan takunkumi a watan disamba da ya wuce.

A halin da ke ciki dai jamiyar Gbagbo dake mulki tayi barazanar janyewa daga cikin shirin zaman lafiyar,tana mai kira da janyewar dakarun Majalisar Dinkin Duniya dana kasar Faransa da suke aikin wanzar da zaman lafiya a kasar.

Magoya bayan Gbagbo a cikin majalisar dokokin kasar sun zargi masu shiga tsakani da wuce gona da iri da nuna isa akan hukumomi masu yancin kansu.