1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana ci-gaba da zanga-zangar nuna adawa da Sarki Gyanendra

April 15, 2006
https://p.dw.com/p/Bv1u

Dubun dubatan masu fafatukar neman demukiradiyya sun gudanar da zanga-zanga a wajen babban birnin kasar Nerpal don yin Allah wadai da mulkin Sarki Gyanendra, wanda ya karbi mulki a bara. A kuma halin da ake ciki ´yan sanda sun yiwa wasu ´yan jarida dukar tsiya. ´Yan jaridar na zanga-zangar nuna adawa da wani matakin murkushe kafofin yada labaru a birnin Kathmandu. Yajin aikin gama gari da ´yan adawa suka kira don tilastawa sarki Gyanendra ya sauka daga kan mulki, ya gurgunta harkokin yau da kullum a kasar ta Nepal. Kimanin ´yan jarida 200 ne suka yi maci a birnin Kathmandu don neman ´yancin ´yan jarida sannan kuma a sako ´yan jaridar da aka kame. ´Yan sanda sun yi amfani da kulake don tarwatsa masu zanga-zanga.