1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana ci-gaban da yin tir da kisan Bhutto

December 28, 2007
https://p.dw.com/p/ChIw

Shugabannin ƙasashen duniya na ci-gaba da yin Allah wadai da kisan gillan da aka yiwa Benazir Bhutto. Shugaban Amirka George W Bush ya bayyana wannan kisa da cewa aiki ne na matsorata, masu tsattsauran ra´ayin waɗanda ke ƙoƙarin yiwa shirin shimfiɗa mulkin demoƙuraɗiyya a Pakistan zagon ƙasa. Shi kuwa babban sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Ban Ki Moon cewa yayi kisan wani aiki ne na rashin imani da nufin janyo rudami a Pakistan.

Ban ya ce:

“Na kaɗu kuma na fusata dangane da kisan da aka yiwa tsohuwar Firaminista Misis Bhutto da kuma sauran fararen hula da aka kashe a wannan harin bam ´yan ta´adda. Ina kira ga hukumomi da su cafke kuma su gurfanad da wadanda suka aikata wannan aika-aika a gaban ƙuliya. Ina maraba da sanarwar kwamitin sulhu wadda ta yi tir da wannnan kisa.”