1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana cigaba da dauki ba dadi a yankin najef da basra a iraq

August 12, 2004

Ruwan Bama bamai a Birnin najef yayi sanadiyar mutuwar mutane 25 a daren jiya a yayin da sama da mutane 75 ne suka mutu a Basra a tsakanin dakarun Amurka da magoya bayan Moqtadar Sadr

https://p.dw.com/p/BvhM
Hoto: AP

Wannan bata kashin kuwa ta faru ne a birnin Kut baya ga Najef inda ake cigaba da dauki ba dadi a tsakanin bangarorin biyu .kamar dai yarda daraktan Asibitin Kut yace yawancin wadanda abun yafi shafa mata ne da kanannan yara .A cewar daya daga cikin manyan jamian kasar ta iraq yace an fara wannan dauki daidai tun daga karfe daya na daren jiya wanda aka kwashe Saonnni ukku ana wannan bata kashi .An dai yi wannan fafatawar ne a lardin Al shakira inda dakarun Amurka ke zargin cewa a nan ne ake da magoya bayan shiawa a lardin baki daya .Bugu da kari kuma anan ne shugaban shiawan Moqtadar sadr keda ofis .Jim kadan bayan wannan fafatawa sai yan tawayen suka kai wani kazamin farmaki a ofishin yan sandan birnin na Kut tare da kashe daya baya ga raunata wasu da dama a cewar Wakar Al bashar daya daga cikin shugabannin yan sandan yankin na Kut .bugu da kari sun kuma cinnawa ofishin wuta .A wata sanarwa data fito daga maaikatar cikin gida ta kasar an cafke a kalla magoya bayan sadr a daren jiya a cikin wannan artabu .Tun daga daren jiya dai dakarun Amurka suka kara kaimi na farautar yan kungiyar mahdi wadanda ke marawa Sadr baya a Najef .Lardin na Al shakira ya kasance wanin dandali na magoya bayan shiawa a kasar ta iraq wanda ya sanya dakarun Amurka yiwa yanmin kawanya .A safiyar nan ta yau dai Yara da Mata da kuma Magidanta sun fito cikin hawaye bisa taannnacin da Amurka ta shinfida a yankin a daren jiya .Ibrahim sultan daya daga cikin mazauna biornin yace a daren jiya suka dunga jin Amon wuta ta sararin samaniya wanda duk wani mai nunfashi a yankin sai da ya tashi tsaye bisa halin rayuwa da yankin ya fada a ciki .Yace a sakamakon wannan bAma baman na daren jiya Asibitin garin ya cika makil da gawarwaki baya ga wadanda suka sami raunika wasu kuwa rai naga hannun Allah ..A can yankin basra kuwa shiawan yankin nsun gargadi mazauna yankin da kada su kuskura su bayar da tallafi ga dakarun Britaniya dake cikin yankin idan kuwa ba haka ba to babu shjakka zasu bakunci lahira .Cikin wadannan jamian kuwa har da yan kwangila da masu yi masu fassara daga Larabci zuwa turanci .To sai dai a jiya mukaddashin Gwamnan lardin na basra yace idan Amurka bata yi hankali ba yankin zai koma tamkar najef idan har basu dakatar da wannan kutsen ba a Najef a nan gaba kadan ..A hannu guda kuma shugaban shiawan kasar ta iraq baki daya Ayatollah Ali Al sistani wanda a halin yanzu ke kwance a gadon Asibiti a birnin londopn bisa cutar bugun zuciya ya nuna bacin ransa na yarda ake cigaba da kutsa kai a najef birnin mafi Tsarki a kasar ..A dangane da haka dai ya bukaci sanya halin ya kamata a tsakanin bangarorin biyu .Ayatollah Al sistani ya tabbatar da wannan matsayinsa ne a wata hira daya gabatar da daya daga cikin magoya bayansa a Najef a yau Alhamis .