1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana dakon sakamakon zaɓe a Kenya

Ibrahim SaniDecember 27, 2007
https://p.dw.com/p/ChBE

An rufe tashohin zaɓe na shugaban ƙasa da kuma na ´yan majalisun dokoki a ƙasar Kenya. Tashe-tashen hankula a lokacin zaɓen ya haifar da asarar rayuka uku, wasu kuma da yawa sun jikkata. Takarar shugabancin ƙasar ta gudana ne, a tsakanin shugaba Mwai Kibaki da kuma Mr Raila Odinga. Shugaba Kibaki na neman yin tazarce ne a karo na biyu a jere. ´Yan takarar biyu sunyi alƙawarin mayar da ilimin sakandare kyauta, a hannu ɗaya kuma da inganta tattalin arziƙin ƙasar. Tun kafin zaɓen na yau, jam´iyyun adawa sun zargi Gwamnati da ƙoƙarin yin maguɗi a wannan zaɓe. Rahotanni sun ce ´yan takarar biyu na kunnen doki, dangane da hasashen lashe wannan zaɓe. A gobe juma´a ake sa ran fitowar sakamakon wannan zaɓe a hukumance.