1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana duba rawa da Faransa ta taka cikin kisan kiyashi na Rwanda

October 24, 2006
https://p.dw.com/p/Buem

A kasar Rwanda a yau wani komiti ya fara zamansa zagaye na farko don duba rawa da Faransa ta taka lokacin kisan kiyashi da akayi a kasar a 1994,tare kuma da duba yiwuwar kaita gaban kotun kasa da kasa.

Komitin dake da alhakin yanke wannan hukunci zai saurari shaidu kusan 25 cikin mako guda,ya hada da masana tarihi,kwararru a fannin sharia da manyan jamian soji na tsohuwar rundunar sojin Rwanda ana kuma sa ran zai mika rahotonsa nan da watanni 6.

Cikin wadanda zasu bada shaida a yau har da jakadan Rwanda a kasar Faransa bayan kisan kiyashin,da kuma tsohon shugaban hukumar leken asiri na kasar a shekar 1993 zuwa 1994.

Komitin zai duba zargin cewa kasar faransa ta bada horo da kuma makamai ga wadanda suka aikata kisan kiyashi a Rwanda,inda mutane kusan 800,000 suka rasa rayukansu cikin kwanaki dari na zubda jini a kasar,ta kuma taimakawa wasunsu suka tsere daga kasar.

Kasar Faransa wadda ta aike da dakarunta zuwa kudu masu yammacin Rwanda a makonni karshe na kashekashen a Rwanda ta karyata wannan zargi.