1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana duba yiwuwar tura dakarun Jamus zuwa Jamhuriyar Demokiradiyyar Kongo

January 14, 2006
https://p.dw.com/p/BvCN

Kungiyar Tarayyar Turai na gudanar da bincike akan tura sojojin Jamus a kasar JDK. Wani kakakin ma´aikatar tsaron Jamus ya tabbatar da haka lokacin wata hira da mujallar Der Spiegel. Kakakin ya ce MDD ta roki KTT da ta tura wata rundunar kundunbala mai sojoji kimanin dubu daya da 500 zuwa Kongo, don su taimaka a hana barkewar sabon yakin basasa. A ranar 29 ga watan afrilu aka shirya gudanar da zaben gama gari karon farko cikin shekaru da yawa a tsohuwar kasar ta Zayya.