1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana fafatawa tsakanin ´yan bindigan Hamas da Fatah

January 27, 2007
https://p.dw.com/p/BuT7
´Yan bindiga dadi daga kungiyoyin Falasdinawa da ba sa ga maciji da juna wato Hamas da Fatah, sun koma fagen fama a Zirin Gaza. Hakan ya zo ne kwana guda bayan da aka kashe akalla Falasdinawa 15 sannan wasu dama suka jikata a wani kazamin fada mafi muni a cikin makonnin nan. Fadan ya sa an dakatar da tattaunawar kafa gwamnatin hadin kan Falasdinawa tsakanin Fatah da gwamnati karkashin jagorancin Hamas. Tun bayan barkewar fadan a ranar alhamis da ta gabata, ´yan bindigan Fatah sun yi garkuwa da ´yan Hamas su 19, yayin da magoya bayan Hamas kuma suka yi awon gaba da ´yan Fatah su 5.