1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana garkuwa da wata Bajamushiya a Irak

November 29, 2005

Ga alamu tun a ranar juma'a da ta wuce ne aka kame wata Bajamushiya domin garkuwa da ita a kasar Iraki

https://p.dw.com/p/Bu3s
Fursinonin da ake garkuwa da su
Fursinonin da ake garkuwa da suHoto: Tagesschau

A jiya litinin ne wani massinja ya mika wa ofishin wani dan jaridar dake aika wa tashar telebijin ta Jamus ARD a birnin Bagadaza kaset din bidiyo dake dauke da bayanai game da Bajamushiyar da ake garkuwa da ita. Hoton ya nuna fursinonin guda biyo da aka daure musu idanuwansu kwance a kasa da kuma wasu dakaru uku dake sa ido akansu. A saboda taka tsantsan ba a nuna hoton gaba dayansa ba ta akwatin telebijin, amma sakon da daya daga cikin masu alhakin garkuwar ya karanto ya kunshi bayani dalla-dalla, inda yake cewar sai fa Jamus ta katse dukkan huldodinta da gwamnatin Iraki, in kuwa ba haka ba za a bindige dukkan fursinonin da ake garkuwa da su har lahira. Sai kuma mummunan laifin da suke zargin bajamushiyar da aikatawa wanda ya shafi ainifin sana’arta ta tone kayan tarihi, inda suke zarginta da laifin satar kayan tarihin kasar Iraki. Kuma ko da yake wannan zargin ba ya da tushe, amma masu alhakin tsare fursinonin akwai ainifin makasudinsu a game da wannan mataki da suka dauka. Domin kuwa ita bajamushiyar dake da shekaru 40 da haifuwa ba bakuwa ba ce a kasar Iraki, saboda tun shekaru 10 da suka wuce ne ta koma da zama a kasar tana mai rungumar musulunci bayan auren wani balarabe da tayi. A baya ga haka ta kann hada kann matakan taimako ga talakawan kasar. Har yau dai ba a san tahakikanin masu alhakin garkuwa da ita ba. Ba kuma wanda ya san alkiblarsu walau ta siyasa ko ta addini. Amma ga alamu sun dade suna shirya wannan danyyen aiki. To sai dai kuma abin da ya jefa jami’ai cikin rudami shi ne bukatarsu ta katse dukkan alaka tsakanin Jamus da Iraki. Saboda a halin da ake ciki yanzu haka babu wata kakkarfar alaka tsakanin kasashen biyu. Jamus na ba da horo ga jami’an tsaron kasar Iraki a ketare, kuma sai daga bisanin nan ne gwamnati ke tsaya wa ‚yan kasuwar dake zuba jari a kasar da yaki yayi kaca-kaca da ita. A fannin al’adu kuwa akwai hadin kai tsakanin Jamus da Iraki domin tono kayayyakin tarihi, kuma mai yiwuwa wannan alakar na da nasaba da garkuwar da aka yi da malamar kayan tarihin, domin kuwa an shirya gabatar da wani mataki na tono kayan tarihin a wani yanki dake kudu da birnin Bagadaza a cikin watan desamba mai kamawa. Tuni dai murna ta koma ciki a game da zaton da aka yi da farko cewar kaddarar garkuwa da fursinoni ‚yan kasashen ketare ba zata rutsa da Jamusawa ba, saboda gwamnatin kasar ta ki ta tsoma hannunta a yakin da aka gabatar kann kasar Iraki. Domin kuwa a kwanan baya sai da aka yi garkuwa da wasu ‚yan jaridar kasar Faransa su uku duk kuwa da cewar Faransar, daidai da Jamus, ba ta da hannu a yakin Irakin.