1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana gudanar da zaɓe a Afganistan

September 18, 2010

Daga fara zaɓen 'yan majalisa dokoki a Afganistan, an fara samun kura-kurai, hakama Taliban ta kai hari a lardin Kandahar

https://p.dw.com/p/PFQ6
Masu zaɓe a AfganistanHoto: DW

A yayin da san'yin safiyar yau aka fara zaɓen 'yan majalisar dokokin ƙasar Afganistan, har an fara jin rohotonnin samun kura-kurai a yadda zaɓen ke gudana. Wani jami'in hukumar kula da koke-koken zaɓen ƙasar Ahmad Zia Rafat, yace akwai ƙorofe-ƙorofen da suka fara samu musamman kan tawadar da ake amfani da ita wajen dangwala ƙuri'a, haka ma wani jami'in hukumar zaɓen ƙasar ya faɗawa manema labarai cewa, daga fara aikin sai suka fahimci tawadar da aka basu akwai sakel. Wannan koke-koken dai sun zone sa'o'i uku da fara zaɓen 'yan majalisar dokokin ƙasar. Sai dai shi kuwa shugaban ƙasar Hamid Karzai ya kira 'yan ƙasar da su pito don kaɗa ƙuri'a. Mutane kimanin miliyan goma da rabi suka cancanci kaɗa ƙuri'a a ƙasar, inda za su zaɓi 'yan majalisar dokoki mai mutane 249. Su kuwa 'yan Taliban da ke adawa da zaɓen sun kai hari da roka a birnin Kabul sa'o'i kafin fara zaɓen. Haka ma bayan an fara zaɓen sun kai hari a wani lardi da ke gabacin ƙasar, inda wani gwamnan lardin ya tsallake rijiya da baya, amma wasu mutanen biyu sun mutu a harin. Wannan zaɓen dai shine ginshiƙin tabbatar da tsarin da zai kai ga picewar dakarun ƙasashen yamma daga Afganistan.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Yahouza Sadissou Madobi