1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana juyayin zagayowar shekara biyu da aukuwar igiyar ruwan Tsunami

December 26, 2006
https://p.dw.com/p/BuWT
Shekaru 2 bayan aukuwar igiyar ruwan nan ta Tsunami, wadanda suka tsira da sauran ´yan´uwa su na kai ziyarar a yankin gabar tekun don tunawa da wadanda wannan bala´i ya rutsa da su. Igiyar ruwan wadda ta auku a ranar 26 ga watan desamban shekara ta 2004, ta halaka mutane dubu 230. Mazauna yankunan sun kunna kyandur tare da yin shiru na mintuna biyu don juyayin wadanda suka rasu. A kuma can lardin Arceh na kasar Indonesia inda bala´i ya fi kamari har yanzu ana fuskantar koma baya a aikin sake gina wannan lardi, sakamakon ambaliyar ruwa da rashin kyawon yanayi. Akalla mutane dubu 167 suka rasu sannan har yanzu dubban mutane ke ci-gaba da zama a gidajen wucin gadi a lardin na Aceh.