1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana kara matsawa masu rikici a Darfur lamba

April 29, 2006
https://p.dw.com/p/Bv0F

Kasashen duniya suna ci gaba da matsin lamba ga bangarorin dake rikici a Darfur,da su hanzarta samarda yarjejeniyar zaman lafiya kafin waadin ranar lahadi da kungiyar taraiyar Afrika ta diban masu.

Shirin na zaman lafiya da masu shiga tsakani na kungiyar suka bullo da shi,yana nufin kawo karshen abinda yan tawayen suka kira watsi da gwamnatin Sudan tayi da yankin nasu.

Akalla mutane 200,000 ne suka rasa rayukansu wasu kuma miliyan 2 suka rasa gidajensu,tun lokacin da rikici ya barke tsakanin yan tawaye da kungiyoyin sojin haya da gwamnati ke marawa baya a 2003.

Har yanzu dai yan tawayen basu mayarda wani martani ba dangane da yarjejeniyar,amma da yawa daga cikin shugabanninsu sun baiyana rashin gamsuwarsu da shi.Gwamnatin Sudan dai ta nuna cewa,a shirye take ta sanya hannu akan yarjejeniyar duk da korafi da rashin gamsuwa da wasu suka nuna.