1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ANA KARA SAMUN YAWAN MASU NUNA KYAMA GA AMIRKA A DUNIYA

YAHAYA AHMEDMarch 17, 2004

Shekara daya bayan afka wa Iraqi da yaki da Amirka ta yi, an gudanad da wani bincike da ke nuna cewa, yawan masu nuna bacin ransu ga manufofin Amirka a duniya baki daya sai kara habaka yake yi. Kafar nan ta PEW RESEARCH CENTERS ta Amirkan ce ta gudanad da binciken a Amirkan da kanta, da kasashe 8 na Turai, a cikinsu har da Jamus da Farransa, da kuma kasashen Larabawa da na duniyar musulmi.

https://p.dw.com/p/BvlE
Masu zanga-zangar nuna adawa ga yakin da Amirka ta afka wa Iraqi
Masu zanga-zangar nuna adawa ga yakin da Amirka ta afka wa IraqiHoto: AP

Sakamakon da binciken ya samo dai, abin ban takaici ne ga Amirka, inji Madeleine Albright, tsohuwar ministan harkokin wajen Amirka, karkashin shugabancin Bill Clinton. Da take gabatad da rahoton da kafar nan ta Pew Research Centers ta buga jiya a birnin Washington, Madeleine Albrigt ta bayyana cewa:-

"Sakamakon dai abin damuwa ne, saboda Amirkawa kadai ne suka yarda cewa yakin da aka yi a Iraqi, don fatattakar kungiyar Al-Qaeda, yana da fa’ida. Abin damuwa ne kuma ganin cewa, a duk sauran kasashen da aka gudanad da binciken, kwarjinin Amirka tamkar kasa amintacciya mai rungumar tafarkin dimukradiyya, sai kara dusashewa yake yi."

Mafi yawan wadanda aka yi musu tambayoyin a Jamus da Faransa da Turkiyya da kuma rabin al’ummomin Birtaniya da na Rasha, sun bayyana ra’ayin cewa, yakin Iraqi dai cikas kawai ya janyo ga manufar yakan ta’addanci. A Jamus da Faransa ne sakamakon bincken ya fi muni. Kashi 82 cikin dari na duk Jamusawa, da kashi 78 cikin dari na Faransawan da aka yi wa tambayoyin ne suka nuna tsarguwarsu ga Amirka. A Birtaniya ma, kasar da ta fi nuna cikakken goyon baya ga shugaba Bush a nahiyar Turai, yawan wadanda suka amince da yakin Iraqin ya ragu da kashi 20 cikin dari, a cikin shekara daya. A kan wannan tsamari da ake ta kara samu tsakanin Amirkan da kasashen Turai dai, Madeleine Albright ta bayyana cewa:-

"Barakar da ake samu tsakanin kasashen yankin Atlantica , wadda yakin Iraqi ya janyo, sai kara fadi take yi."

Amma binciken kuma ya nuna cewa, a kasashen da ke adawa da afka wa Iraqin da yaki ma, mafi yawan jama’a ne suka bayyana ra‘ayin cewa hambarad da Saddam Hussein da aka yi, zai kyautata makomar `yan kasar Iraqi.

Sai dai wannan ra’ayin kasashen Turai kawai ya shafa. Jama’ar kasashen muslumi ba sa goyon bayan ra’ayin. A lal misali, a kasar Jordan, kashi 70 cikin dari na wadanda aka yi musu tambayoyin ne suka yi imanin cewa, halin rayuwar `yan kasar Iraqi ya kara lalacewa yanzu fiye da lokacin Saddam Hussein. A Pakistan kuma, kashi 61 cikin dari ne suka bayyana wannan ra’ayin. Al’umman kasashen Larabawa dai na alamta yin watsi da manufofin siyasar Amirka ne, da nuna zumunci da amincewa da Usama bin Laden. Kamar dai yadda binciken na Pew Research Centers ke nunawa, kashi 65 cikin dari na al’umman Pakistan ne ke nuna gamsuwarsu da bajintar shugaban na kungiyar Al-Qaeda. A Jordan kuma, kashi 55 cikin dari na al’umman kasar ne ke goyon bayan fafutukar bin Laden din. Kai har a Turkiyya ma, inda al’umman kasar da dama suka rasa rayukansu a hare-haren kunan bakin waken da aka kai a birnin Istanbul, kashi 31 cikin dari na jama’ar kasar ne ke ganin cewa, harin kunan bakin waken da ake ta kai wa Amirkawa a Iraqi, abu ne mai kyau.

Andrew Kohut, darektan cibiyar ta Pew, wadda ta gudanad da binciken, ya bayyana cewa hare-haren kunan bakin waken da aka kai a Turkiyya da Rasha a shekarar bara, ya sa wasu `yan wadannan kasashen sun nuna goyon bayansu ga shirin yaki da ta’addancin da Amirka ke jagoranci. Amma gaba daya dai, a kasashen musulmi, wannan shirin ko kadan ba ya samun amincewar jama’a.