1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana kirga kuri'u a zaben shugaban kasar Laberiya

December 27, 2017

An fara kirga kuri'u a zaben shugaban kasar Laberiya zagaye na biyu inda za a tantance gwani tsakanin tsohon shahararren dan wasan kwallon kafa na duniya George Weah da kuma mataimakin shuagban kasa Joseph Boakai.

https://p.dw.com/p/2pydQ
Liberia Wahlen
Hoto: Reuters/T. Gouegnon

An fara kirga kuri'u a zaben shugaban kasar Laberiya zagaye na biyu da ya gudana a wannan Talata da ta gabata cikin tsanaki da kwanciyar hankali, a wannan kasa da a baya ta yi fama da yakin basasa na tsawon shekaru. 'Yan takara biyu da suka fafata su ne tsohon shahararren dan wasan kwallon kafa na duniya George Weah da kuma mataimakin shuagban kasa Joseph Boakai.

Duk wanda ya samu nasara zai maye gurbin Shugaba Ellen Johnson Sirleaf mai garin wanda wadda ta mulki kasar ta Laberiya da ke yankin yammacin Afirka na tsawon shekaru 12, kuma take zama mace ta farko da aka zaba ta jagoranci wata kasa a nahiyar Afirka.

Masu saka idon kan zabe sun yaba da yadda zaben na Laberiya ya gudna a cikin har da tsohon Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya wanda ya jagoranci wata kungiya mai mazauni a Amirka. Cikin kwanaki masu zuwa ake sa ran hukumar zaben Laberiya za ta ayyana wanda ya lashe zaben na shugaban kasa.