1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana maraba da yakar cin hanci a Najeriya

Usman Shehu Usman/ASAugust 12, 2015

'Yan Najeriya na cigaba da nuna goyon bayansu ga yakin da Shugaba Buhari ke yi da cin hanci da rashawa a kasar.

https://p.dw.com/p/1GENp
Niger Buhari Issoufou
Hoto: DW/M. Kanta

Goyon bayan da Buhari ke samu daga bangarorin kudanci da arewacin kasar kan yakin da ya daura da masu cin hanci dai alamu ne da ke nuna cewa 'yan Najeriya sun gaji da irin yanayin da kasar ta shiga na yin sama da fadi da dukiyar baitulmali wanda hakan ya jefa su cikin yanayi na rashin cigaba.

Kasashen duniya ma da ke hulda da Najeriya sun yi na'am da matakan shugaban kasar na yakar cin hanci. Lamarin na matukar karfafa musu gwiwa domin dama can suna zumudin shiga Najeriya don zuba jari amma matsaloli irinsu rashin gaskiya da cin hanci na dakushe wannan yunkuri nasu.

UN Nigeria Präsident Goodluck Jonathan
Al'ummar Najeriya na zargin gwamnatin tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan da satar dukiyar kasa.Hoto: picture-alliance/United Archives/WHA

Tuni mutane irinsu Olaf Schumeser, jagoran reshen bankin kasar Jamus na Commerzbank a Najeriya ya fara cewar ''alamar da ke fitowa daga fadar gwamnatin Najeriya ta na samun yabo. Zan iya tabbatar da cewa a yanzu muna shirye don kulla yarjeniyoyi bisa ka'idar kasa da kasa"

USA Muhammadu Buhari und Barack Obama in Washington
Kasashen duniya ciki har da Amirka za su taimakawa Najeriya wajen gano kudadenta da aka sace.Hoto: Reuters/K. Lamarque

Sai da wani abu da ke kawo shakku kan tafiyar gwamnatin Buhari kawo yanzu shi ne tsaikon da aka samu wajen nada ministoci domin kuwa sai an samu ministoci kafin kamfanoni da sauran masu hulda da Najeriya su iya samun wadanda za su tattauna da su.

Wannan batun na jan kafa wajen fidda ministocin dai ya sanya masana tattalin arziki a Najeriya kamar Dr. Bashir Kurfi na jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya cewa ya kyautu a ce ya zuwa yanzu an samu ministoci duba da tsawon watanni biyu da aka samu bayan zabe kafin a kai ga rantsar da Muhammadu Buhari a matsayin shugaban kasa.