1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana neman Blaise Compaore ruwa a jallo

Abdourahman HassaneDecember 22, 2015

Burkina Faso ta gabatar da takardar sammacin kasa da kasa don kama hamɓararen shugaba Compaore kan zarginsa da hannu a kisan tsohon Shugaba Thomas Sankara

https://p.dw.com/p/1HRfg
Burkina Faso Mali-Abkommen in Ouagadougou
Hoto: AHMED OUOBA/AFP/Getty Images

Hakan kuwa na zuwa ne a daidai lokacin da masu yin bincike a Faransa na gwajin ƙwayoyin halittu suka ce bincikken da suka yi a kan gawar tsohon shugaban bai ba su damar gano dalilan mutuwarsa ba.

An dai soma gudanar da binciken ne a ƙarshen watan Maris na wannan shekara bayan faɗuwar gwamnatin Blaise Compaoré a cikin watan Oktoba da za wuce. Wanda ya zo a kan karagar mulki a rana 15 ga watan Oktoba na shekara ta 1987 a juyin mulkin da ya yi wanda a cikinsa shugaba Thomas Sankara da wasu na kusa da shi su 12 suka mutu.

Tun farko dai a wani gwajin ƙwayoyin halittu da aka yi, ya nuna cewar gawar ta Thomas Sankara harbin harsassai sun yi mata kaca-kaca, to amma daga bisani bayan an miƙa gawar zuwa Faransa a wani asibitin bincike na 'yan sanda da ke a Marseille, ƙwararrun sun ce babu wani sakamako da suka samu a cikin binciken da suka yi a kan wani ɗan gutun ɓangare na gawar.

Burkina Faso Mariam Sankara
Mariam SankaraHoto: Getty Images/AFP/A. Ouoba

To sai dai lauyar da ke kare iyalan Thomas Sankara Benewende Sankara ta ce alƙalai masu gudanar da bincike suna da cikakkun hujojin ci ga da yin shari'a.Kuma daga cikin waɗanda aka kama a kan wannan al'amari har' da Janar Gilbert Diendéré mutumin da ya yunƙurin kifar da gwamnatin wucin gadi ta Burkina a cikin watannin da suka gabata,kana kuma gwamnatin ta gabatar da sammacin kama tsohon shugaban ƙasar wato Blaise Compaoré wanda ke yin gudun hijira a Cote d'Ivoire. Noufou Zougmoré wani dan jarida ne mai yin bincike wanda ke yin na cike da shaku game da cewar ko hukumomin na Cote d'Ivoire za su iya miƙa mista Blaise kana kuma ya ƙara da cewar.

''Haƙiƙa mun san irin rawar da Blaise Compaoré ya taka wajen zuwan Alassane Ouatara a kan ragamar mulki, ba mamaki ya ƙi ba da haɗin kai, amma dai a yanzu kotu ta kutsa kai a cikin wannan shari'a ko ba jima ko ba daɗe zai fuskanci shari'a.''

Gwamnatin dai ta Burkina Faso ta riga ta sanar da hukumomin na Cote d'Ivoire sannan kuma ta shaidawa hukumar 'yan sanda ta ƙasa da ƙasa watau Interpol. Mariam Sankara ita ce mai ɗakin tsohon shugaban ƙasar da aka yi wa kisan gilla.

Thomas Sankara Präsident Burkina Faso Ankunft in Harare 1986
Thomas SankaraHoto: Getty Images/AFP/A. Joe

'' Na yi murna da farin ciki da naji a ƙarshe an gabatar da takardar sammaci ta ƙasa da ƙasa domin kama Blaise Compaoré, abin da muka yi ta fata shekara da shekaru kenan, domin na san ba shakka yana da hannu a cikin kisan da aka yi wa mijina, muna fata zai bayyana a gaban kotu domin amsa tambayoyin alƙalai kan wannan wani abu ne da muka daɗe muna jiran gani.''

Wannan batu dai da alama zai ƙara dagula hulɗa tsakanin ƙasashen biyu,bayan da a cikin makwanni na baya-baya nan aka bangaɗo wasu bayanai na sauran wayoyin tarho wanda ke nuna cewar kakakin majalisar dokokin na Cote d'Ivoire Guillaume Soro na da hannu a yunuƙurin juyin mulkin da ya ci tura wanda Janar Dendiéré ya yi a cikin watan Satumbar da ya gabata.