1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana neman Grace Mugabe bisa laifin cin zarafin wata mata

Ramatu Garba Baba MNA
August 15, 2017

Uwargidan shugaban kasar Zimbabuwe Grace Mugabe ta mika kanta ga hannun hukumomin Afirka ta Kudu bayan an zarge ta da laifin cin zarafin wata mata a birnin Johannesburg.

https://p.dw.com/p/2iHPQ
Simbabwe Robert und Grace Mugabe
Hoto: Getty Images/AFP/A. Joe

Uwargidan shugaban kasar Zimbabuwe Grace Mugabe ta mika kanta ga hannun hukumomin Afirka ta Kudu bayan an zarge ta da laifin cin zarafin wata mata a birnin Johannesburg, matar mai suna Gabriella Engels ta shigar da kara a gaban kotu a sakamakon dukan da ta ce ta sha a hannun Grace Mugabe na ba gaira ba dalili. A cewar matar al'amarin ya auku ne a lokacin da ta je wani otel don ganawa da dan Grace Mugabe a ranar Lahadin da ta gabata. Ga dukkan alamu dai hakan bai yi wa Uwargidan Mugaben dadi ba, abin da ya sa ta far ma ta da duka. Engels ta bayyana takaicinta kan yadda masu tsaron lafiyar Misis Mugabe suka nuna halin ko-in-kula a yayin da take shan dukan.

A wani lokaci a wannan Talata ake sa ran Uwargidan Robert Mugabe za ta bayyana a gaban kotu don kare kanta daga wannan zargin. Babban jami'in 'yan sanda na birnin Johannesburg Fikile Mbalula ya ce Misis Mugabe tana basu hadin kai kuma za a yanke mata hukunci in har aka same ta da laifin da ake zarginta a kai, rahotanni na nuni da cewa tuni misis Mugabe ta isa kasar Zimbabuwe ba tare da amsa kiran kotun ba.