1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana nuna damuwa kan shirye-shiryen zabe a Nijar

Abdoulaye Mamane Amadou/ MNANovember 11, 2015

Kungiyar kare hakin dan Adam ta ANDDH ta nuna tsananin damuwarta kan shirye-shiryen zabe a Nijar, musamman ma batun rajistar sunayen masu zabe.

https://p.dw.com/p/1H49p
Niger Mahamadou Issoufou und Hama Amadou
Hoto: BOUREIMA HAMA/AFP/Getty Images

A yayin wani zaman taro da hadaddiyar kungiyar kare hakin dan Adam a Nijar ta ANDDH ta yi ne, kungiyar ta soki yadda wasu hukumomi masu ruwa da tsaki a harkar zabe ke tafiyar da ayyukan shirye-shiryen zaben da ake shirin gudanarwa a farko farkon shekarar 2016. Kungiyar ta yi zargin rashin natsuwa da sakaci a wajen aikin rajistar sunayen masu zabe da ke zama daya daga cikin ginshikin duk wani 'yanci da walwala wajen zabe da ke ga 'yan kasar na fita domin jefa kuri'a.

ANDDH ta ce kundin rajistar sunayen masu zabe tattare yake da kurakurai wadanda har ta kai ga kungiyar kasancewa cikin damuwa da daurin kai dangance da abinda ke faruwa a hukumar ta CEFEB wacce ke aikin rajistar ta sunayen masu zabe.

Farfesa Djibril Abarchi shi ne shugaban hadaddiyar kungiyar ta ANDDH da ya yi karin haske.

"Ba su hangi nauyin da kasa ta aza masu ba wanda ka cewa zaka je ka tarar da shi har a gida ka rubuta sunanshi, ba cewa za ka yi shi zo ba, ba ka iya cewa a'a babu sunanka. Har wadanda aka kirga ma ba su cikin girgam din. Yanzu ne ake ga zabe don duk wanda ya yi kuwa ya ce yana da mutane da yawa amma ba su cikin girgam din zabe kenan baka da kowa."

Suka kan kundin rajistar zabe

Ko baya ga kungiyar ta ANDDH wasu kungiyoyin farar fulla da na 'yan adawa sun sha yi wa sabon kundin rajistar sunayen masu zaben mummunar suka.

Niger Niamey Opposition
Wani jerin gwanon 'yan adawa a YamaiHoto: DW/M. Kanta

Na baya-bayan nan shi ne taron gangamin 'yan adawar kasar da suka bukaci da a gudanar da kyakkyawan bincike ga kundin don kauce wa kurakurai a ranaikun zabe. Kurakuran kuma da kan iya zama ummal-haba'isin fitina inji 'yan adawa.

Sai dai da take mayar da martani kan korafe-korafen hukumar CEFEB mai aikin rubuta sunayen masu zabe, a ta bakin kakakinta Abdourahmane Assouma cewa ta yi hukumar na aiki gadangadan domin ganin ta damka kundin a cikin lokaci.

"Mu aikin namu ba mu ganin cikas a ciki, domin aikin namu tare muke yinshi da 'yan adawa da 'yan masu mulki da wadanda suke 'yan baruwanmu. Idan har a waje wasu sun ce ga yadda muke tafiyar da aikin namu, to ina ganin bai san abinda ke faruwa ba ko kuwa yana da wata manufa."

Ko baya ga batun kundin rajistar sunayen masu zabe kungiyar ta ANDDH ta sake waiwaye kan batun samun damar shiga a kafafen yada labaru mallakar gwamnati. Kungiyar ta yi kakkausar suka kan yadda ake fifita wasu jam'iyyun siyasa fiye da wasu wajen samun sararin shiga kafafen yada labarun mallakar gwamnatin domin yada manufofinsu na siyasa. Kungiyar ta kare hakkin dan Adam ta ce duk wata tattakala irin wannan na iya kawoma demukradiyyar Nijar tarnaki da koma baya inji Shugabanta Farfesa Djibril Abarchi.

"Idan har an ce sanarwar da kake yi zuwa ga 'yan kasa, idan wannan in ya yi minti biyar wancan minti 10 za a bashi, ba a yi adalci ba, kenan ba tafiya daya ake ba kamar a ce dawaki ne za a jera don sukuwa sai a saka wa daya dabaibiya, shi kuma dayan a barshi a ce a tafi a yi sukuwa."

Hukuma ba ta fifita wani kan wani

Niger Wahlen Politik Stimmen Auszählung
Hoto: DW/M. Kanta

Sai dai a duk lokacin da aka yi batun rashin samun damar shiga kafafen yada labaru mallakar gwamnati jama'a kan nuna dan yatsa ne izuwa hukumar koli mai kula da kafofin yada labaru ta CSC, wanda kuma shugabanta Malam Abdourahmane Ousman ya yi tsokaci kan wannan batu yana mai cewa.

"'Yan adawa ko 'yan siyasa suna da 'yancin su fadi abinda suka ga dama, amma abinda nike so shi ne ina so jam'iyyar siyasa daya da ta fito ta bada hujjar da rannar da ta aje takarda a nan wajen hukumar kasa mai kula da sadarwa don a bata 'yancin magana cikin rediyo da talabijin na gwamnati kuma mu muka hana musu wannan 'yancin."

Sanarwar ta kungiyar ANDDH na zuwa ne yayin da wata tawaga ta musamman da kungiyar kasashe renon Faransa ke wata ziyarar aiki a birnin Yamai, inda suke ganawa da hukumomin kasar masu ruwa da tsaki a harkar zabe. Ko baya ga hukumomi, tawagar kungiyar za ta gana da 'yan siyasa da shugabannin addinai. Duk wannan kuwa saboda nuna damuwa da yadda Nijar ke shirin gudanar da zabubbukanta a sabuwar shekara mai kamawa.