1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ANA SAMUN HABAKAR FATAUCIN MAGUNGUNAN JABU A DUNIYA.

Yahaya AhmedJanuary 21, 2004
https://p.dw.com/p/BvmS
A nan Jamus dai, jami'an Hukumar Kiwon Lafiya, na sa ido kwarai wajen ganin cewa, kamfanonin sarrafa magunguna da kuma masu kasuwancinsu, na bin ka'idoji masu tsananin da aka ajiye musu, don kiyaye lafiyar jama'a. Amma duk da hakan, a wasu lokutan, akan sami wasu magungunan jabu da suke shigowa kasuwannin nan kasar. Sai dai, ba irin wadanda ake samunsu a wasu kasashen da ba su da tsauraran matakan bin diddigin asalin magungunan ba ne. Wani babban sifeton `yan sandan ciki na nan Jamus, Richard Karl Mörbel, wanda ya dade yana shugabacin wani rukuni mai bin diddigin `yan fasa kwaurin magungunan jabu na kasa da kasa, zuwa kasuwannin Turai, ya bayyana cewa, saboda tsananta bin ka'idoji da ake yi a nan Jamus, sai masu sarrafa magungunan jabu sun kware kwarai, suna kuma da sarkakkun na'urori, kafin su iya kwaikwayon irin magungunan da ake da su a nan kasar.
Ko ta yaya aka sarrafa magungunan jabun dai, duk masu yin wannan danyen aikin, manufa daya suke bi: wato ta son kudancewa nan take. Dokokin Jamus dai sun tanadi hukunci mai tsanani kan duk wadanda aka kama da kwaikwayon sarrafa wani magani na asali da kuma yin kasuwancinsa. Amma a ganin jami'an `yan sandan ciki, kamata ya yi a kara tsananta hukuncin ma, a mai da laifin daidai da na kisa, saboda shan irin wadannan magungunan, na iya janyo asarar rayukan jama'a
A halin yanzu dai, an tsara kundin wasu sabbin dokoki, sai dai ba a zartad da su a majalisa ba ne tukuna. Tsarin dokokin kuwa sun tanadi hukuncin dauri a gidan yari har zuwa shekaru 10, a kan duk wanda aka samu da laifin sarrafa ko kuma kasuwancin magungunan jabu a nan Jamus. A da can dai, mafi yawan `yan fasa kwaurin magungunan jabun, a kasashe masu tasowa ne suka fi tura kayayyakinsu. Amma a halin yanzu, ana ta kara samun habakar wannan sumogan a kasashen Turai da Amirka. Hukumar Lafiya Ta Duniya, ta bayyana cewa kusan kashi 30 cikin dari na magungunan jabun da ake sarrafawa a duniya, yanzu akasashe masu arzikin masanna'antu ake fataucinsu. Amma har ila yau dai, a kasashen Afirka da na Kudu Maso Gabashin Asiya ne aka fi jin illolin da wannan danyen aikin ke janyowa a jika. Musamman a wuraren da aka fi yawan cututtuka kamarsu Tibi, da Maleriya da AIDS, an fi tura irin wadannan magungunan jabun. Akwai dai hanyoyi da dama da wasu marasa imani ke bi wajen gudanad da fataucin magungunan. Babban sifeton `yan sandan ciki, Richard Mörbel, ya kara bayyana cewa.-
"Akwai wata hanyar da da `yan sumogan ke bi wajen shigowa da magungunan jabu nan kasar. A lal misali suna iya samo su ne daga kasashe kamarsu Malesiya, su biyo da su ta gabashin Turai zuwa nan Jamus. Har ila yau dai, akwai wasu kuma, wadanda idan an ba da taimakon sahihan magunguna ga kasashe masu tasowa kamarsu na Afirka, sai su tare magungunan a hanya, su sake juyowa da su zuwa nan Turai su sayar. A karshe dai, wadanda aka nufa da magungunan, kamarsu masu cutar AIDS a Afirka Ta Kudu, ba sa samunsu, saboda rashin imanin da wadannan miyagun mutanen ke nunawa." Hukumar Lafiya Ta Duniya, ta kiyasci cewa, a halin yanzu kusan kashi 60 cikin dari na magungunan da ake harkokinsu a duniya, na jabu ne, kuma ba su ma da tasiri na sinadarin da ya kamata su kunsa. Wasu kamfanonin sarrafa magunguna a nan Turai dai na koakarin kare kayayyakinsu da wasu alamu na musamman, wadanda za su yi wuyan kwaikwayo. Kamar yadda sifeto Mörbel ya ci gaba da bayyanarwa:-
"A halin yanzu dai wasu kamfanoni na amfani da alamu daban-daban wajen kare magungunansu da kuma bambanta su da na jabu. An fi dai yin amfani da wadannan alamun ne a kan magunguna masu tsadar gaske. Amma a nan ma, akwai haddin da kamfanonin ba za su iya wucewa ba, saboda idan kudin sarrafa magungunan ya tashi, dole ne a sami hauhawara farashinsu a kasuwanni."
A halin yanzu dai za a iya cewa, kowa ke son ya sha sahihin magani na kwarai, sai fa ya tanadi aljihu mai zurfi.