1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana ta ƙara gano gawawwakin waɗanda annobar ta Tsunami ta ritsa da su a Indonesiya.

July 19, 2006
https://p.dw.com/p/Buq0

Jami’an ƙasar Indonesiya, sun ce yawan mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon tashin igiyar ruwan nan ta tsunami a kan tsibirin Java a ran litinin da ta wuce, ya tashi zuwa sama da ɗari 4. Wata girgizar ƙasa a ƙarƙashin teku, mai ƙarfin awo 7 da ɗigo 7 a kan mizanin Richter ne ta janyo annobar. Igiyar ruwar, wadda ta kai tsawon mita 2 ta ragargaz duk wasu matsugunai da ke gaɓar tekun tsakiyar tsibirin na Java.

Gwamnatin Indonesiyan dai ta ce har ila yau, ba ta da isassu, kuma ingantattun na’urori, don gano ɓarkewar irin wannan annobar a cikin lokaci.