1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana ta ƙara samun hauhawar tsamari tsakanin Ƙungiyoyin Fatah da na Hamas a zirin Gaza.

May 18, 2006
https://p.dw.com/p/Buxm

Shugaban Falasɗinawa Mahmoud Abbas, ya umarci ƙungiyar Hamas da ke jagorancin hukmar Falasdianawan, da ta janye dakarunta daga titunan garin Gaza. Rahotanni sun ce Abbas ya tura dubban jami’an tsaro zuwa zirin na Gaza, don su tabbata da doka da oda. Hakan kuwa ya biyo bayan girke dakaru kusan dubu 3 ne a zirin da ƙungiyar Hamas ɗin ta yi jiya laraba, duk da adawar da shugaban Falasɗinawan ke yi da kafa wani sabon rukuni na jami’an tsaro a yankunan Falasɗinawan. Rahotanni dai sun ce dubban ’yan sandan Falasɗinawan na sintiri a sabon shacin tsaro da ƙungiyar Hamas ɗin ta ƙirƙiro a garin Gaza.

A Gaɓar Yamma kuma, mun sami rahotannin cewa, hauhawar tsamari tsakanin ƙungiyoyin Fatah da na Hamas ɗin na ta kara haɓaka, inda wani rukunin ’yan bindigan Fatah, ya kewaye wani ginin da mataimakin Firamiyan Falasɗianawan, Nasser Shaer, ke taro a ciki.