1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana takaddama akan sabon sarkin Kuwait

January 18, 2006
https://p.dw.com/p/BvBj

A kasar Kuwai wani dan majalisar dokoki ya zargi wasu takwarorinsa da kokarin ture sabon sarkin da ya gaji wanda yarasu.

Ahmad Al saadun wanda daya daga cikin fitattun yan majalisar kasar ne ya zargi wasu yan majalisane da suke cewa sabon sarkin sai ya karanta rantsuwar hawa sarauta kamar yadda take sidira zuwa sidira a kundin mulkin kasar,duk kuwa da shakkun da ake nunawa na ganin cewa sabon sarkin bazai iya jurewa ya karanta rantuswar ba har zuwa karshenta saboda rashin cikakkiyar lafiyar sa.

Dan majalisar ya soki masu kafewa akan sai shi Sheik Saad al Abdullah al sabah yayi rantsuwar kamar yadda take da cewa suna son ture shine saboda wata manufa ta siyasa kawai.

Akan hakanne kuma wasu suke bada shawarar da a takaita rantsuwar yadda zai iya karantawa.

A dangane da halin da ake ciki ne na wannan takaddama iyalan sarautar suka gudanar da wata ganawa inda suka tattauna akan batun da kuma nadin sabon yarima mai jiran gado.