1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana zargi gwamnati Kamaru da take hakkin fursunoni

Gazali Abdou Tasawa
July 20, 2017

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta zargin jami'an tsaron kasar Kamaru da hallaka mutanen da ake tsare da su a gidajen kurkukun kasar a bisa zargin kasancewa 'yan kungiyar Boko Haram.

https://p.dw.com/p/2gsvW
Kampf gegen Boko Haram Nigeria
Hoto: picture-alliance/dpa/Ngala Chimtom

Kungiyar ta bayyana wannan zargi ne a cikin wani rahoto da ta wallafa inda ta ce firsunonin na mutuwa ne a sakamakon tsananin akubar da jami'an tsaron kasar ta kamaru ke gallaza masu a gidajen kurkukun da ake tsare da su a kasar.

Kungiyar kare hakkin dan Adam din ta Amnesty International ta bayyana cewa ta tattauna da mutane 101 wadanda suka tabbatar da cewa jami'an rundunar zaratan sojojin yaki da Boko Haram ta kasar ta Kamaru ta  BIR wato brigade d'Intervention Rapid a Faransance sun gana masu azaba a gidajen wakafi da ake tsare da su a asirce da ma a cibiyar Hukumar leken asirin waje ta kasa ta DGRE tsakanin watan Maris na shekara 2013 zuwa Maris na 2017.

Soldat Kamerun Maschinengewehr West Afrika
Hoto: picture-alliance/dpa/T.Graham

Kuma 32 daga cikin wadannan mutane 101 sun kwarmata wa Kungiyar ta Amnesty cewa da idanunsu sun sha shaida mutuwar wasu daga cikin abokanin zaman kason nasu a wadannan cibiyoyi biyu na BIR da DGRE. Samira Daoud jami'ar Kungiyar ta Amnesty International reshen kasar ta Kamaru wadda ta ce tabbatar da cewa matsalar tana da girma.

Kungiyar ta Amnest International ta bayyana Cibiyar Salak ta rundunar yaki da Boko Haram ta BIR  a matsayin wacce ta yi fice wajen azabtar da fisrunonin. Kuma rahoton kungiyar ya ce akwai yiwuwar Faransa da Amirka na da masaniya kan barnar da jami'an tsaron kasar ta kamaru ke aikatawa a cikin wannan cibiya domin ta mallaki faifayin bibiyo da ke nuni da cewa jami'an tsaron kasar ta Faransa da na Amirka na yawan kasancewa a cikin wannan cibiya ta Salak.

Nigeria - Soldaten an der Grenze zu Niger
Hoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Yanzu haka dai Kungiyar ta Amnesty ta gargadi mahukuntan kasar ta Kamaru ta su amince cewa akwai matsalar domin kuwa a yau akwai tarin hujjoji da ke tabbatar da ukubar da jami'an tsaron kasar ta kamaru ke gana wa firsunoni kana su dauki matakan dakatar da tsare mutane a wuraren sirri da kuma gana masu azaba. Kazalika Kungiyar ta Amnisty ta ce ta tuntubi ofisoshin jakadancin kasashen Amirka da Faransa domin su gudanar da bincike na neman sanin ko har jami'an nasu suna da masaniya kan azabar da jami'an tsaron kasar ta Kamaru ke ganawa firsunonin da ake tsare da su a bisa zargin dangantaka da Kungiyar Boko Haram.