1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana zargin kamfanonin Jamus da samun hannu a taɓargazar ba da cin hanci da rashawa a harkokin kwangilar makamai a Afirka Ta Kudu.

Yahaya AhmedJuly 4, 2006

A Afirka Ta Kudu, wata taɓargaza ta kunno kai a harkokin ba da kwamgilar makamai, inda ake tuhumar kamafnonin ƙetare, musamman na Jamus da samun hannu a zargin ba da cin hanci da rsahawar da ake yi musu.

https://p.dw.com/p/BtzQ
Shugaba Thabo Mbeki, lokacin yaƙin neman zaɓe a Afirka Ta Kudu.
Shugaba Thabo Mbeki, lokacin yaƙin neman zaɓe a Afirka Ta Kudu.Hoto: AP

Tun cikin 1999 ne wata ’yar siyasar jam’iyyun adawa, Patricia de Lille, ta bukaci a gudanad da bincike kan bai wa kamfanonin Jamus kwangilar makaman soji da aka yi, duk da cewa ba su cika ƙa’idojin da aka shimfiɗa ba. A cikin wata fira da ta yi da maneman labarai, Patricia de Lille ta bayyana cewa:-

„Ba daidai ba ne a ce, an bai wa wani kwangila wanda tun da farko ma, bai cika ƙa’idojin da muka ajiye ba. Akwai dai maguɗi a wannan harkar. Kuma bisa dukkan alamu, an shirya wannan maguɗin ne bayan da tsohon mataimakin shugaban ƙasa da kuma shugaban ƙasar na yanzu Thabo Mbeki, ya kai ziyara a Jamus. Akwai dai dalilin da ya sa aka bai wa Jamus wannan kwangilar. Tun da daɗewa ne nake tuhumar wani ɗanyen aiki a nan.“

Ban da dai shekarar 1999n, a shekara ta 2001 da 2003 ma, sai da ’yar majalisar ta sake bukatar gwamnatin Afirka Ta Kudun ta gudanad da bincike kan wannan batun. Amma a duk waɗannan lokutan, inji de Lille:-

„Sai suka yi watsi da bukatar. Ce mini aka yi, ban san ma ainihin yadda al’amura ke wakana ba, balantana ma in fahimci ko me ake ciki. A yanzu dai, a hankali ana samun haske a kan lamarin. Ina godiya ga kafofin yaɗa labaran Jamus, waɗanda suka sake tono wannan batun.“

Babu shakka, a harkokin kasuwancin makamai dai, kusan a ko yaushe, sai an ba da cin hanci da rashawa. Oditocin ƙasar Afirka Ta Kudun dai sun gano cewa, a lokacin ba da kwangilar, akwai ababa da dama da ba a sami haske a kansu ba. Sabili da haka ne dai suka ba da shawarar, a sake gudanad da cikakken bincike kan tsarin ba da kwangilar makaman ƙasar ma gaba ɗaya. To amma, sai kuma ministan shari’ar ƙasar ta ƙi bai wa kwamitin da aka naɗa izinin gudanad da aikinsa.

Duk da hakan dai, wata kotun Afirka ta Kudun, ta yanke wa wani mai bai wa gwamnatin ƙasar shawara kan harkokin kuɗi, ɗaurin shekaru 15 a gidan yari, saboda samunsa da laifin da ta yi, na karɓar cin hanci daga wani kamfanin Faransa. Shi dai wannan jami’in, wani tsohon shugaban reshen jam’iyyar ANC ne a majalisar dokokin ƙasar, wanda aka ce ya karɓi kyautar motar marssandi, don ya taimaka wajen samun kwangilar. A ƙarshen wannan watan ne kuma, tsohon mataimakin shugaban ƙasar Jacob Zuma, shi ma zai bayyana gaban kotu, saboda tuhumarsa da ake yi na karɓar cin hanci da rashawar. Gaba ɗaya dai, ana hashen cewa an kashe kusan Euro biliyan 7 a harkar kwangilar makaman na Afirka Ta Kudu, kuma kuɗaɗe masu ɗimbin yawa daga wannan adadin, sun bi hanyar cin hanci ne da rashawa.

’Yar siyasar jam’iyyun adawar Afirka Ta Kudun Patricia de Lille ta bayyana gamsuwarta da binciken kamfanin nan Thyssen-Krupp na nan Jamus, da hukumomin shari’an tarayya ke yi, saboda tuhumar guje wa biyan haraji da kuma ba da cin hanci da rashawa da ake yi masa. Ta kyautata zaton cewa, wannan zai ƙara ba da haske, kann binciken da ake gudanarwa a Afirka Ta Kudun da kanta:-

„Har ila yau dai, ina fatar cewa Afirka Ta Kudu za ta ba da haɗin kai ga masu gudanad da bincike na Jamus. Kuma ina fatar gwamnatin ƙasarmu ma za ta faɗaɗa nata binciken.“