1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ANATA FUSKANTAR KAI KARE HARE A IRAQI

July 26, 2004
https://p.dw.com/p/Bvhm

Har yanzu tsugune bata kare ba a dauki dai dai din da yan sari ka noke keyi a can kasar Iraqi,domin kuwa a yau ma wani dan kunar bakin wake ya afkawa wata mota dake shake da boma bomai kusa da sansanin sojin amurka a garin Mosul dake arewacin Bagadaza,abinda kuma ya hallaka mutum uku ciki harda wata mata da yaro guda da kuma wani mai gadi.

Wannan harin dai shine mafi kazanta tun bayan harin da aka kai a makon daya gabat wanda ya hallaka sama da mutum 50 ya kuma raunata da dama abinda kuma ake zaton kungiyar nan ta Abu Musab Alzarqawi ce ke da alhakinsa.

Kakakin rundunar sojin na amurka Capt Angela M:Bowman ta tabbatar da cewar wata mota ce shake da boma bomai dake da nauyin kimanin mm 122 da kuma gurneti mai nauyin mm60 yayin da wannan dan kunar bakin wake ya afkamata kuma nan take wadannan bomabomai suka tarwatse,abinda kuma bayan hallaka mtum uku da yayi sojin amurka uku sun samu muggan raunuka.

Yansari kanoke sun aika da wani babban jamin maaikatar harkokin cikin gida na Iraqi lahira a safiyar yau din nan,yayin da suka kai hari akan motar dake dauke da shi.Rahotanni dai sun tabbatar da cewar nan take ya mutu tare da masu tsaron lafiyar sa su biyu.

Wannan alamari dai kullum shine abinda ake ci gaba da fuskanta a kasar ta Iraqi tun bayan da aka hambarar da gwamnatin shugaba Saddam Hussain yantakife ke ta kai munanan hare hare kann wurare dabam dabam kamrsu hukumomin yansanda da jamian tsaro da kuma uwa uba kann sojojin amurka.

Har ila yau yantawayen sun bada sanarwar yin garkuwa da wasu yan kasar Pakistan guda biyu dakewa sojojin amurka aiki,saboda kasar ta pakistan na tunanin turawa da sojojin ta zuwa kasar ta Iraqi don su marawa sojojin amurka baya.

Kasar Pakistan mai yawan musulmi kimanin miliyan 150 tana goyon bayan amurka na yaki da ta’addanci amma kuma a hannu guda batayi maraba da mamayar da amurkan ta yiwa kasar Iraqi.ba.

Wani gidan talabijin din larabawa mai suna Pan Arab ya nuna wani kaset din video dake nuna hotunan wadannan mutane dauke da wata sanarwa daga yantakifen dake bayyana cewar zasu hallaka su amma basu fadi lokacin aiwatar da kashe sun ba.

Gwamnatin Pakistan ta tabbatar da cewa wadannan mutanen da akai garkuwa dasu yan kasar tane,kuma tun a makon daya gabata,aka kasa gano inda suke.wadannan mutanen dai sune.Raja Azad dan shekara 49 Enginiya ne,sai kuma Sajad Naeem dan shekara 29 direba.

Wannan garkuwa da yantakifen keyiwa yan kasashen waje a akasar ta Iraqi wani abune da hausawa kance a tauna tsakuwa don aya taji tsoro,Wannan kungiya ta yantakife dai dakewa kanta kirari da cewar Islamic Army in Iraq ta kuma yi garkuwa da wani matukin motar wani kamfanin dake gudanar da kwangiloli,inda ta lashi takobin fille masa kai idan har kamfanin da yakewa aiki bai fice daga cikin kasar ta Iraqi ba.Ance dai ba’a san maci tuwo ba sai miya ta kare.

BELLO UMAR