1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ancimma yarjejeniyar sulhu akan Somalia

June 22, 2006
https://p.dw.com/p/Bu6Q
A karo na farko,gwamnatin rikon kwaryan da kotunan musulunci dake adawa da juna a Somalia,sun amince da juna a ganawarsu kai tsaye a yau a kasar Sudan.A wata rubutacciyar yarjejeniya da bangarorin biyu suka rattaba hannu akai,sun amince da sake komawa zagayen tattaunawar ta biyu a khartum a ranar 25 ga watan yuli.Ministan harkokin waje na Somalia Abdullahi Shekh Ismail da shugaban gamayyar kotunan musulunci na kasar,Mohammed Ali Ibrahim sun rungumi juna ,bayan rattaba hannu a yarjejeniyar.A yau ne dai tawagar bangarorin biyu a karkashin jagorancin kungiyar gamayyar kasasshen larabawa,suka gana da juna a birnin Khartum,akokarin da ake na warware rikicin da somaliyan ke ciki na shekaru masu yawa.

Sudan ce ta dauki nauyin karban bakuncin bangarorin biyu ,tare da kiran taron kasashen larabawa ,domin kare sake barkewan sabon yaki a somalia,wadda ta gaza samun zaunanniyar gwamnati cikin shekaru 15 da suka gabata.A rubutacciyar yarjejeniyar ta yau dai,gwamnatin rikon kwaryar ta amince da gamayyar kotunan musuluncin amatsayin yantacciyar kungiya,a yayinda a hannu guda kuma kungiyar ta amince da da kasancewa gwamnatin rikon ,bisa kaida.