1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Angela Merkel ta isa China

May 21, 2006
https://p.dw.com/p/BuxM

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta isa kasar Sin a yau lahadi a kan wata ziyara da zata mayarda hankali kann batutuwan ciniki da harkokin kula da kare hakkin bi adama.

Merkel tana jagorantar tawagar mutum 40 wadanda suka hada da manyan yan kasuwa,da kuma ministocin tattalin arziki dana sufuri na Jamus.

Kasar Sin dai itace babbar abokiyar kasuwancin Jamus a nahiyar Asiya,saboda haka zasu tattauna akan batun kasuwanci,ana kuma sa ran Merkel zata bukaci shugabanin kasar ta Sin da su janyo hanjkalin Iran ta dakatar da sarrafa sinadarin uraniyum da take yi.

Shugabar gwamnatin ta Jamus zata kuma gana da shugaban darikar katolika na Sin a kokarinta na samarda walwalar addini a kasar ta Sin.