1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Angela Merkel ta kare matsayin EU a kan 'yan gudun hijira

April 8, 2016

Shugabar gwamnatin tarayyar Jamus Angela Merkel ta yi kokarin kare matsayin da kungiyar EU ta dauka kan yarjejeniyar da suka cimma kan mayar da 'yan gudun hijirar nahiyar zuwa Turkiya.

https://p.dw.com/p/1ISI5
Berlin Bundeskanzlerin Merkel PK zu Terroranschläge in Brüssel
Hoto: picture-alliance/dpa/K. Nietfeld

Yunkurin kare matsayin kungiyar tarayyar Turan da Merkel ke kokarin yi na zuwa ne a yayin da kungiyoyin kare hakkokin bil adama ke ci gaba da sukar lamirin matakin.

A yayin da take ganawa da wakilan da ke lura da harkokin 'yan gudun hijira a Berlin Shugabar ta jaddada cewar yarjejeniyar da Turkiya wacce ta kunshi 'yan gudun hijirar Siriya sama da miliyan biyu ita ce mafuta ga magance matsalar kwararar 'yan gudun hijirar.Kazalika Angela Merkel ta kara da cewar:

''Ina ganin ya yi dai dai kan yadda aka cimma yarjejeniyar da Turkiya ta hanyar raba daukar nauyin matsalar,Turkiya ta karbi 'yan gudun hijirar Siriya sama da miliyan 2 gami da karin wasu daga wasu kasashen Turai ,Ina ganin babu wani abin kace nace,a inda EU ta za tallafawa kasar da kudade.''