1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Angela Merkel ta tashi zuwa rangadin kasashen China da Japan

August 26, 2007
https://p.dw.com/p/BuD5
Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel ta tashi zuwa gabashin nahiyar Asiya inda zata fara wani rangadi na mako guda a kasashen China da Japan. Ana sa rai zata karfafa aniyar ta ta yaki da dumamar yanayi a tattaunawar da zata yi da shugabannin kasashen biyu. jami´ai a birnin Berlin sun ce Merkel ba zata yi wata-wata ba wajen tabo muhimman batutuwa kuma masu wuya a China ba wato kamar kare ´yancin dan Adam da na ´yan jarida. Gabanin ta tashi SG ta Jamus ta ce dangantaka tsakanin Jamus da China sun yi kyau saboda haka ba zata yi shakkan tabo wadannan batutuwan da ake takaddama a kansu ba. Jim kadan gabanin tashinta mujallar Der Spegel ta rawaito cewa wasu ´yan China masu leken asiri na bayannan komputa sun yi amfani da wani shirin leken asiri da ake kira Trojan inda suka kutsa cikin nau´rorin komputa na gwamnatin Jamus, ciki har da ta fadar shugabar gwamnati. To amma China ta yi watsi da wannan zargi tana mai cewa bai da tushe bare makama.