1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Angola: Joao Lourenço ya sha alwashin yaki da cin hanci

Salissou Boukari
July 26, 2017

Dan takaran neman Shugabancin kasar Angola da ake sa ran zai canji shugaba Jose Eduardo Dos Santos, ya sanar da aniyarsa ta yaki da cin hanci da rashawa idan har ya hau kan karagar mulkin kasar.

https://p.dw.com/p/2h991
Angola Wahlkampf Joao Lourenco MPLA
Dan takarar neman shugabancin kasar Angola Joao Lourenço, da mai dakinsa Ana Dias Lourenço yayin yakin neman zabe.

Lourenço ya yi wadannan kalamai ne ya yin wani taron gangami na jam'iyyarsa ta MPLA ta shirya a yakin neman zaben da aka soma na zaben 'yan majalisar dokokin kasar da zai gudana a ranar 23 ga watan Augusta mai kamawa.

Shidai Joao Lourenço mai shekaru 63 da haihuwa, shi ne kan gaba cikin jerin sunayen 'yan takara na jam'iyyar ta MPLA ta shugaban kasa Jose Eduardo Dos Santos wanda ya zabi kin sake tsayawa takarar neman shugabancin kasar bayan da ya shafe shekaru 37 ya na mulkin kasar ta Angola.

Kundin tsarin mulkin kasar ta Angola dai bai tanadi zaben shugaban kasa ba, sai dai jam'iyyar da ta samu rinjaye a zaben 'yan majalisar dokoki ce ke da shugaban kasa. Baya ma ga yaki da cin hanci, dan takaran jam'iyya mai mulkin ya sha alwashin rarraba arzikin kasar daidai wadaida ga sauran yankunan, da kuma bunkasa harkokin kasuwanci idan har ya yi nasara.