1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Angola ta fitar da jadawalin zaben gama gari

Salissou Boukari
April 25, 2017

Majalisar Jamhuriyar Angola wadda shugaban kasar José Eduardo dos Santos ke jagoranta ta fitar da yadawalin zabukan kasar, inda ta tsayar da 23 ga watan Agusta mai zuwa a matsayin ranar zabe.

https://p.dw.com/p/2bqei
Wahlen in Angola
Hoto: DW/N. Sul d'Angola

Yayin wani taron manema labarai da ya jagoranta ne, babban mai shigar da kara na gwamnatin kasar ta Angola Joao Maria de Sousa, ya ce bisa shawarar shugaban kasa, babbar majalisar jamhuriya ta kaddamar da jadawalin zabukan gama gani na kasar ta Angola. Wannan mataki zai kawo karshen wa'adin mulki na shekaru 30 da shugaba Dos santos ya yi yana mulki.

Shugaban na Angola dos Santos mai shekaru 74 da haihuwa, na a kan karagar mulkin kasar ne tun daga shekara ta 1979, inda ya ce ba zai sake neman wani wa'adin mulki ba. A watan Febirairu da ya gabata ne dai jam'iyyarsa ta MPLA ta zabi ministan tsaron kasar na yanzu José Lourenço a matsayin wanda zai gaje shi. Masu adawa da shugaban kasar dai na zarginsa da yin abun da ya ga dama da dukiyar kasar.