1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Annobar kwalara a Guine Bissao

Yahouza sadissouAugust 25, 2005

Passara hira da Ministar kiwan lahia ta Guine-Bissao Maria Odete Semedo a game da cutar kwalara da ta bulla a kasar.

https://p.dw.com/p/BvaC

Cutar kwalara da ta bullo tun watan juni da ya wuce a kasar Guine-Bissao, na ci gaba da hadasa mace- macen jama´a.

Abokan aikin mu, na sashen Portuganci a Redio DW,sun yi fira da ministan kiwon lahia- ta Guine-Bissao, inda su ka fara da tambayar ta yawan mutanen da su ka kamu da cutar, da kuma wanda su ka rasa rayukan su, daga bullowar ta, ya zuwa yanzu.

Minista Maria OdeteSemedo ,ta bayana cewa, a jimilce mutane dubu takwas da dari tara da bakwai su ka kamu, kuma kawo yanzu dari da saba´in sun riga mu gidan gaskiya.

A tambayar da su yi mata na matakan da gwamnati ta dauka domin magance matsalar, ta yi nuni da cewa:

Majalisar ministoci ta haramta taruwar jama´a, a wuraren suna ko bukkukuwa, da tarruruka makamantan su.

Dalilin daukar wannan mataki, shine na takaita cudayar mutane, domin ta wannan hanya ce, cutar kwalara, ke samun damar kara yaduwa.

Minista Maria, ta bayana cewa daga samun yancin kan kasar Guine Bissao, kawo yanzu wannan itace cutar kwalara mafi tada hankali da kasar ta fuskanta.

A shekara ta 1986 an yi cutar inda mutane 200 su ka kamu kuma 57 daga cikin su su ka kwanta dama.

Haka zalika ,a shekara ta 1996 an maimaita ta, a wannan lokaci mutane 167 su ka kamu 161 su ka mutu.

Daro daga jerin matakan da gwamnati ta dauka na dakile cutar akwai padakar da jama´a.

A halin yanzu, mu na aiki kafada da kafada da matasa da sojoji da kuma kungiyoyi, a cikin birane da karkara domin waye kan jama´a akan mahimmanci tsabatar jiki, da ta kaya da ta mahali.

Bisa dukan alamu muna ga hakar zata cimma ruwa, amma duk da haka inji minista Maria Odete, gwamnati ta yi kira ga kasashen dunia masu hannu da shuni, da su taimako cikin gaggawa.