1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Annobar sinadarin Darma a Zamfara

June 7, 2010

Jami'an lafiya a Zamfara sun ƙaddamar da shin gaggawa na kula da lafiyar waɗanda suka kamu da gubar Darma.

https://p.dw.com/p/NkHR
Hoto: Christiane Kaess

Hukumomin lafiya a jihar Zamfara dake arewacin Nigeria sun kafa cibiyoyin bada agajin gaggawa domin kula da mutanen da suka kamu da wata gubar Dalma yawancin su ƙananan yara sakamakon haƙar ma'adanin zinare ba bisa ƙa'ida ba.

A halin da ake ciki yanzu hukumomin lafiya a jihar ta Zamfara tare da haɗin gwiwar maaikatar lafiya ta tarayyar Nigeriar da kuma wasu hukumomin lafiya na ƙasa da ƙasa da suka haɗa da hukumar lafiya ta duniya da kuma cibiyar yaƙi da cutattuka masu yaɗuwa ta Amirka sun duƙufa wajen shawo kan wannan al'amari.

Kwamishinan lafiya na jihar Zamfara Dr Saad Idris yace mutanen da suka kamu da gubar suna aiki haƙar ma'adanin ne ba tare da sanin gwamnati ba. To sai dai shin menene dangantakar Dalmar da kuma zinare ? Kwamishinan lafiyar Dr Saad Idris yace a cikin dutsen akwai sinadari da yawa wadanda suka hada da Darma ko kula Lead a turance akwai Tama da Azurfa da Asenic da dai sauran su. Masana kiwon lafiya sun ce sinadarin na Dalma yana da matuƙar haɗarin gaske musamman idan aka ci ko kuma aka shaƙe shi.

Goldgräber auf Madagaskar
Yara masu haƙara ma'adanai.Hoto: Dominique Thébaud

Ya zuwa yanzu dai rahotanni sun ce mutane kimanin 300 ne suka rasu yawancin su ƙananan yara sakamakon kamuwa da gubar ta Dalma da suka ɗauka a lokacin da suke tonar zinaren ba bisa ƙa'ida ba. Amma ko mai ya sa hukumomin na Zamfara ba su ɗauki matakin yiwa tubkar hanci ba har sai da abin ya kai ga hasarar rayuka ? A nan kwamishinan lafiya na jihar Dr Saad Idris yayi bayani da cewa : Tun da muka tantance wannan abu mun dau mataki. Ina son ka san da cewa mu ne muka je, ma'aikata ce da jami'ai na da sauran jami'ai da suke taimaka mana kamar MSF muka je wurin, kuma wannan ginar sinadaran ana yi ne tun 1945 a nan jihar Zamfara waɗanda suke wannan aiki kuma suna yi ne a ɓoye

Ya zuwa yanzu dai rahotanni sun ce wannan annoba ta faru ne a wasu ƙauyuka guda biyar dake cikin ƙananan hukumomin Anka da kuma Bukuyum dake kusa da Gusau babban birnin Jihar ta Zamfara. A ta bakin kwamishinan lafiyar Dr Saad Idris yace gwamnati ta killace wurin ta kuma hana cigaba da hakar ma'adani a wannan wurin : Mun dau mataki mun hana wannan sannan mataki na biyu shi ne mun samo magani yanzu, mun riga mun fara kwasar yaran nan daga wurin muna kai su babban Asibiti na garin Bukuyum sannan kuma za mu kai wasu babban Asibiti na garin Anka da yake kananan hukumomi biyu da Anka da Bukuyum aka sami wannan matsala.

A small farm of maize
Hoto: DW

Ganin cewa damuna na ƙara gabatowa, domin kaucewa yaɗuwar wannan sinadarin Dalma mai guba, gwamnati ta ƙudiri aniyar kwashe ƙasar wurin domin maye gurbinta da wata tsabtatacciyar ƙasa mai kyau a cewar kwamishinan lafiyar : In sha Allahu mun fara kai kayan kwasar wannan ƙasa, da yake Allah ya sa ƙididdiga ta nuna mana cewa abin bai zurfi ba sosai, za mu kwashe ƙasa ta sama-sama a ƙauyukan, da yake ƙananan ƙauyuka ne ba manyan garuruwa bane, amma duk da haka na san aiki ne babba za mu kwashe ƙasar nan sannan kuma mu ɗebo wata mai kyau mu zuba.

Baya ga wannan wata babbar fargaba da jama'a ke baiyanawa, ita ce  yiwuwar sinadarin ya yi naso zuwa rijiyoyin mutane a cikin gidaje da kuma gurbata ruwan da suke sha. Sai dai kwamishinan lafiyar Dr Saad Idris yace gwamnati ta yi la'akari da wannan tana kuma ɗaukar matakin da ya dace : Ruwan shan su ma za'a ƙara tsabtace shi idan akwai rijiyoyi da suke buɗe za mu rufe su mu tabbatar da cewa mun yi musu irin waɗannan Famfuna na tuƙatuƙa yadda idan sun sha ruwa ba za'a sami wata matsala ba.

Ɗaya daga cikin likitocin dake jagorantar aikin gaggawa na kula da lafiyar jama'ar da wannan abu ya shafa Dr Sani Gwarzo ya ce za su horar da jami'an kiwon lafiyar yankin ƙarin dabarun kula da kiwon lafiya tare kuma da faɗakar da al'uma yadda za'a sami cimma nasarar da ake buƙata.

Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala

Edita : Halima Balaraba Abbas