1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Annobar wutar daji a California.

October 23, 2007
https://p.dw.com/p/C15u

Wutar daji dake ci ba ƙaƙkƙautawa ta tilastawa dubban jamaá a kudancin California yin ƙaura daga gidajen su. Rahotanni sun ce wutar wadda ke ƙara ruruwa sakamakon iska mai karfi dake kaɗawa ta ƙone gidaje masu yawa. A ƙalla mutum ɗaya ya rasa ransa wasu maíakatan kashe gobara su goma shida kuma sun sami raunuka. A halin da ake ciki hukumomi sun gargadi ga mutane fiye da 250,000 wadanda gidajen su ke kusa da yankin da wutar ke ci su ƙaurace domin kare lafiyar su. Jamián jihar California sun buƙaci ɗauki daga yan kwana-kwana na maƙwabtakan jihohi. Gwamnan Jihar California Arnold Schwarznegger ya sanar da dokar ta baci inda ya buƙaci taimakon gaggawa ga alúma.