1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Anyi kira ga membobin NATO su kara dakarunsu A Afghanistan

November 28, 2006
https://p.dw.com/p/BuZs

Yayinda shugabannin kungiyar tsaro ta NATO suka hallara a Riga kasar Latvia,sakatare janar na kungiyar Jaap de Hoop Scheffer ya roki kasashen kungiyar da su kara yawan sojojinsu zuwa kudancin Afghanistan.

Kasancewa sojojin Burtaniya,Canada dana Holland a kudancin da kuma dakarun Amurka a gabashu sun janyo janyo ci gaban hare hare.

Shugaban kasar Amurka dai ya bukaci kassahen na NATO dasu amsa wannan bukata da komandojin kungiyar sukayi.

Anashi bangare ministan tsaro na Jamus Franz Josef Jung yace babban abinda zai samarda nasara a Afghanistan shine sake gine kasar ba tilasata kwantar da tawaye ba.

A halinda ake ciki kuma wasu sojin NATO 2 sun rasa rayukansu wani kuma ya samu rauni a lokacinda bam ya fashe kusa da wata motar su a kusa da Kabul.