1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Anyi suka ga shawarar ministan tsaro na Jamus akan Darfur

November 30, 2006
https://p.dw.com/p/BuZk

Anyi suka ga shawarar ministan tsaro na Jamus Franz Josef Jung na aikewa da sojojin jamus zuwa yankin Darfur na kasar Sudan.

Shugaban majalisa mai tsatsauran raayi Volker Kauder yace wannan shawara ba zata karbu ba,yace bai dace ba a tattauna wannan batu ba tare da an tuntubi sauran bangarori na gwamnatin kasar ba.

Kauder yace halinda ake ciki a yankin Darfur,abu ne mai tsanani saboda haka bai dace ba a yada jita jita da zasu tada tsammanin abinda ba zai yiwuwa ba.

Ministar kula da harkokin ci gaba Heidi Marie Wieczorek Zeul dai ta baiyana goyon bayanta ga wannan shawara ta Jung.

Jung dai tun farko yace Jamus ba zata yi watsi da duk wata bukata ta Majalisar Dinkin Duniya na aikewa da dakarunta zuwa Darfur ba.