1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An ci tarar 'yan PDP a shariar zaben gwamnan Plateau

Abdullahi Maidawa Kurgwi/ YBOctober 26, 2015

Hukumar da ke sauraren kararakin zabe a jihar Plateau ta ce jama'iyyar APC ce ke da nasara a zaben gwamnan jihar da aka yi ranar bakwai ga watan Afrilu da ya gabata.

https://p.dw.com/p/1GuYf
Nigeria Oppositionspartei APC
Alamar jam'iyyar APC a NajeriyaHoto: DW/K. Gänsler

Tun hasali ma dai dan takarar gwamnan jihar Plateau a tutar jam'iyyar PDP, Senata Gyang Pwajok, shi ne ya shigar da kara inda ya kalubalanci zaben Barista Simon Lalong, na jama'iyyar APC a zaben gwamnan da aka yi cikin wata Afirilun bana.

A zaman yanke hukunci da aka yi ranar Litinin din nan, Alkalai uku ne suka yi zaman karkashin jagorancin mai sharia Johnson Candida, inda mai sharia Candida ya ce jam'iyyar PDP a shedu 10, da suka gabatar wa hukumar babu wata sheda kwakwkwara da ke da tushe ballantana makama, kuma ma dukkan bayanai da shedun da suka bayar bayanai ne da ke cin karo da juna, don haka alkalin ya yi watsi da karar da PDP ta shigar kana ya yi tarar kudi Naira dubu 50, da za'a bai wa kowane bangare cikin bangarori uku, da ke cikin karar, sun kuwa hada da hukumar zabe, da jama'iyyar APC da kuma shi kan shi dan takarar gwamnan Simon Lalong.

Bayan an tashi a zaman shariar daya daga lauyoyin APC Lira Joseph, ya nuna gamsuwa da matakin kotun, daya kuwa daga cikin lauyoyin PDP bayan neman ya ce wani abu ya gaza cewa komai.

Buhari Nigeria-Wahl 2015
Takardun zabe a NajeriyaHoto: APC

Zaman shariar da aka yi cikin matakan tsaro, mai sharia Candida dai ya shafe sa'oi fiye da biyar ne yana karanta kundin hukuncin da ke kunshe cikin warka 108.

Shi kuwa Yusha'u Mazadu, wani dan jam'iyyar APC ne a jihar Plateau ya ce tun farko suna da cikakkun shedu da koda a kotun koli ne za su yi nasara.

To bayan yanke hukuncin dai babu labarin wata tarzoma, ko tashin hankali, face kawai 'yan jama'iyyar APC ne suka karade birnin Jos da ababen hawa suna bayyana farin cikinsu.

Karte Nigeria mit den Bundesstaaten Adamawa, Bauchi und Plateau
Taswirar Najeriya na nuna jihar PlateauHoto: DW